Iran’s Foreign Minister, Abbas Araghchi, has issued a strong challenge to former United States President, Donald Trump, over the issue of deploying American troops to Iran.
Araghchi stated that if the United States truly possesses the military strength it claims, then Trump should act on his words by sending troops into Iran to reopen the strategic Strait of Hormuz.
According to him: “If you are truly brave, send your troops to Iran as you claimed. Stop the rhetoric and show action.”
This statement comes amid escalating tensions between Iran and the United States, particularly over the Strait of Hormuz, a critical global oil transit route.
Political analysts warn that such remarks could further intensify the conflict and increase instability across the Middle East region.
HAUSA
Ministan harkokin wajen ƙasar Iran, Abbas Araghchi, ya yi kakkausar kalubale ga tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, kan batun shigar da sojojin Amurka cikin Iran.
Araghchi ya bayyana cewa, idan har Amurka na da ƙwarewa da ƙarfin da take ikirari da shi, to ya kamata Trump ya cika maganarsa ta hanyar tura sojoji zuwa Iran domin buɗe mashigar ruwa ta Mashigar Hormuz.
A cewarsa: “Idan kai jarumi ne, ka tura sojojinka zuwa Iran kamar yadda ka faɗa. Ka daina yawan surutu, ka nuna aiki a aikace.”
Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takaddama mai tsanani tsakanin Iran da Amurka, musamman kan muhimmancin mashigar Hormuz, wacce ke ɗaya daga cikin manyan hanyoyin safarar man fetur a duniya.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa irin waɗannan kalamai na iya ƙara rura wutar rikici, tare da haifar da sabon yanayi na tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
0 Comments