An kashe sojan Isra'ila a Kudancin Lebanon

Sojojin Isra’ila sun ce an kashe wani sojansu yayin fafatawa a kudancin Lebanon.

Isra’ilar ta kuma sanar da cewa wasu sojojin sun samu munanan raunuka inda aka kai su asibiti domin samun kulawar likita.

Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan yadda aka kashe sojan ko kuma inda arangamar ta faru ba.

Post a Comment

0 Comments