Trump: We Will End the Iran War Within Weeks
Donald Trump, former President of the United States, has stated that his country is determined to bring an end to the ongoing conflict with Iran within a short period, whether or not a formal agreement is reached.
Trump said he intends to scale down military strikes against Iran, emphasizing that the conflict could come to an end within the next two to three weeks.
According to him, Iran is now under new leadership, which he described as more approachable, less hardline, and more pragmatic compared to previous leaders.
However, he acknowledged that the United States has not succeeded in taking control of the Strait of Hormuz — a strategically vital route that plays a crucial role in global oil supply.
Reports indicate that the conflict has led to a rise in global crude oil prices on Wednesday, April 1, 2026, amid concerns over potential supply shortages.
Despite this, Trump expressed confidence that prices will stabilize in the near future.
He is also expected to deliver a televised address to the American public, providing further details on the situation, according to reports from BBC.
HAUSA
Trump: Za mu kawo ƙarshen yaƙin Iran cikin makonni kaɗan.
Donald Trump, tsohon shugaban ƙasar Amurka, ya bayyana cewa ƙasarsa na da niyyar kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Iran cikin ɗan gajeren lokaci, ko da kuwa an cimma yarjejeniya ko akasin haka.
Trump ya ce yana son rage hare-haren da ake kai wa Iran, yana mai jaddada cewa rikicin zai zo ƙarshe cikin makonni biyu zuwa uku masu zuwa.
A cewarsa, yanzu Iran na ƙarƙashin sabbin shugabanni waɗanda ya bayyana a matsayin masu sauƙin mu’amala, ba masu tsattsauran ra’ayi ba, kuma sun fi magabatansu sassauci da fahimta.
Duk da haka, ya amince cewa Amurka ba ta samu nasarar ƙwace mashigar Hormuz daga hannun Iran ba — wani muhimmin wuri da ke da tasiri sosai ga harkokin man fetur a duniya.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya haifar da tashin farashin ɗanyen mai a yau Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2026, sakamakon fargabar ƙarancin mai a kasuwannin duniya.
Sai dai Trump ya bayyana cewa yana sa ran farashin zai daidaita nan ba da jimawa ba.
Ana sa ran zai gabatar da muhimmin jawabi ga al’ummar Amurka ta kafar talabijin domin yin ƙarin bayani kan halin da ake ciki, kamar yadda rahotannin BBC suka tabbatar.
0 Comments
Drop your thoughts What do you think about this news?