IRAƘI TA FARA SHIRYE-SHIRYEN JANA'IZAR JAGORA SHAHID SYED ALI KHAMENEI; ANA SA RAN MUTANE MILIYAN 10 ZUWA 15 ZA SU HALARTA
Bagadaza, Iraƙi — Hukumomin Iraƙi sun fara manyan shirye-shirye domin gudanar da jana'izar Jagora Shahid Syed Ali Khamenei, wadda ake hasashen za ta kasance ɗaya daga cikin manyan tarukan jana'iza mafi girma a tarihin yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran mutane tsakanin miliyan 10 zuwa 15 daga sassa daban-daban na duniya za su halarci jana'izar, lamarin da ya sa hukumomin Iraƙi suka fara ɗaukar matakan tsaro da shirye-shiryen ba da hidima tun kafin ranar taron.
Shirye-shiryen sun biyo bayan ziyarar Ministan Harkokin Wajen Iran, Dakta Abbas Araghchi, wanda ya gana da manyan jami'an gwamnatin Iraƙi da kuma gwamnonin Najaf, Karbala da Bagadaza domin tattauna yadda za a gudanar da taron cikin tsari.
Gwamnonin Najaf da Karbala sun bayyana cewa an tattara dukkan hukumomin tsaro, lafiya, sufuri da sauran hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da cewa miliyoyin mahalarta sun samu cikakkiyar kariya da kulawa.
Bayanai sun nuna cewa za a fara jana'izar ne daga Haramin Imam Ali (A.S.) da ke Najaf a ranar 8 ga Yuli, sannan a ci gaba da jerin bukukuwa da tarukan ta'aziyya a Karbala, Kazimiyya da Samarra.
Hukumomi sun kuma sanar da cewa an tanadi motocin sufuri, wuraren masauki, abinci, ruwan sha da cibiyoyin lafiya domin sauƙaƙa wa dimbin al'ummar da ake sa ran za su halarta.
Masu sa ido kan al'amuran yankin sun bayyana cewa idan adadin mutanen da ake tsammani ya halarta, jana'izar za ta kasance ɗaya daga cikin manyan tarukan da suka fi tara jama'a a tarihin Iraƙi.
✍️ Muhammad Balaa Afuwa
0 Comments
Drop your thoughts What do you think about this news?