1. Iran ta bayyana martanin da ta bai wa shawarwarin Amurka a matsayin kyakkyawar aniyar ta ta warware rikicin da ke tsakanin su. Jami’an Iran sun ce martanin ya fi karkata ne kan kawo Æ™arshen yaÆ™e-yaÆ™e da rikice-rikicen yankin, musamman na Lebanon, da kuma nemo hanyar sasanta saÉ“anin da ke tsakaninta da Washington. Haka kuma an tattauna batun mashigar Hormuz da shirin nukiliyar Iran, tare da buÆ™atar a cire dukkan takunkuman da aka kakaba mata baki É—aya. Iran ta jaddada cewa dole ne a samu tabbatattun hanyoyi masu garanti wajen cire takunkuman, tare da tabbacin Æ™asa da Æ™asa cewa duk wata yarjejeniya da za a cimma za a aiwatar da ita yadda ya kamata. Jami’an Æ™asar sun ce an tsara wannan martani ne bisa manyan muradun Iran bayan tattaunawa da Æ™asashen yankin.
2. Tehran ta ce idan Amurka ta nuna mutumtawa a saƙon Iran, tattaunawar za ta shiga wani sabon mataki cikin gaggawa. Ta ƙara da cewa yanzu komai yana hannun Washington ne.
3. Rundunar Sojin Iran ta sanar da cewa jiragen FPV marasa matuÆ™i sun zama muhimmin ginshiÆ™i a sabon tsarin yaÆ™inta bayan yaÆ™in kwanaki 12. Ta bayyana cewa an riga an kafa Æ™wararrun Æ™ungiyoyin sarrafa waÉ—annan jirage a kowace rundunar briged mai aiki. Hukumomi sun tabbatar da cewa, tare da tallafin cibiyoyin samar da kayan yaÆ™i da Ma’aikatar Tsaro, babu wata matsala wajen samar da jiragen FPV ko makamansu. Rahotanni sun nuna cewa an samar da dubban jiragen kunar-baÆ™in-wake a watannin baya, yayin da yanzu hankali ya koma wajen Æ™ara horas da sabbin masu sarrafa su da kuma inganta Æ™warewarsu a fagen daga.
4. Rundunar Sojin Iran ta sanar da harbo wani jirgin leƙen asiri marar matuƙi a yankin kudu maso yammacin ƙasar.
5. Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya tattauna ta waya da takwaransa na Holland, Caspar Veldkamp, inda suka tattauna dangantakar ƙasashensu da kuma sabbin sauye-sauyen diflomasiyya da halin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki.
6. Haka kuma Abbas Araghchi ya yi tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Masar, Badr Abdelatty, kan halin da yankin ke ciki da kuma tattaunawar Iran da Amurka da Pakistan ke shiga tsakani a kanta.
7. Sabon jakadan Iran zuwa Vietnam, Akbar Qasemi, ya gana da Abbas Araghchi kafin tafiyarsa zuwa Hanoi. A yayin ganawar ya bayyana shirinsa na ƙarfafa alaƙa tsakanin Tehran da Hanoi tare da faɗaɗa haɗin gwiwa a fannoni kamar siyasa, tattalin arziki, kasuwanci da yawon buɗe ido. Araghchi ya jaddada muhimmancin bunƙasa dangantakar ƙasashen biyu a dukkan fannoni.
8. Abbas Araghchi ya kuma tattauna da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, kan sabbin ci gaban tattaunawar Iran da Amurka ta hanyar shiga tsakani na Pakistan. Haka nan ya yi tattaunawa da Firayim Minista kuma Ministan Harkokin Wajen Qatar, Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, inda suka duba halin da yankin ke ciki da kuma yunƙurin diflomasiyya da ake ci gaba da yi.
9. Rahotanni sun ce daga cikin shawarwarin Iran a tattaunawar akwai buÆ™atar kawo Æ™arshen takura mata da kuma tabbatar da cikakkiyar ‘yancin fitar da man fetur nata. Tehran ta kuma nace cewa duk wata yarjejeniya da Amurka dole ne ta haÉ—a da dakatar da yaÆ™i kai tsaye da zarar an sanar da ita, tare da tabbacin rage tashin hankali a Lebanon. Iran ta É—auki batun tsagaita wutar Lebanon a matsayin É—aya daga cikin manyan sharuÉ—É—anta da ba za ta sassauta ba. Sauran buÆ™atun sun haÉ—a da cire takunkuman Amurka, sakin kuÉ—aÉ—en Iran da aka daskarar, da kuma soke takunkuman OFAC da suka shafi sayar da man Iran. Haka kuma Tehran ta gabatar da shawarar kula da mashigar Hormuz a Æ™arÆ™ashin wata sabuwar yarjejeniya ta fahimtar juna. Rahotanni sun ce shirin ya haÉ—a da ci gaba da tattaunawa na kwanaki 30 bayan dakatar da rikici domin kammala sauran bayanai, tare da É—aukar matakai daga É“angarorin biyu domin gwada yadda Amurka take da niyyar cika alÆ™awuranta. Ana ci gaba da tattaunawar a rubuce ta hanyar shiga tsakani na Pakistan.
10. Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana muhimman batutuwa guda goma da suka shafi Tekun Fasha da mashigar Hormuz. Ya bayyana kasancewar sansanonin sojin Amurka a yankin Tekun Fasha a matsayin babban tushen rashin tsaro da rikice-rikice a yankin. Ya kuma ce sansanonin Amurka ba su da ƙarfin tabbatar da tsaron kansu balle na yankin baki ɗaya. A cewarsa, makomar yankin ita ce Tekun Fasha ya samu yanci daga tasirin Amurka, wanda zai kasance tushen ci gaba da wadata ga ƙasashen yankin. Iran ta jaddada cewa ƙasashen yankin suna da makoma guda da ke haɗa su ta hanyar Tekun Fasha da Tekun Oman. Haka kuma ta yi watsi da ci gaba da kasancewar sojojin ƙasashen waje a yankin.
Iran ta bayyana matakan da take É—auka a Tekun Fasha a matsayin wani É“angare na sabon tsarin siyasa da Æ™arfi da ke kunno kai a yankin da ma duniya baki É—aya. Ta kuma nuna cewa rawar da take takawa wajen kula da mashigar Hormuz na da muhimmanci ga tsaron yankin. Tehran ta ce hana amfani da Hormuz domin cutar da yankin ko anfani da ita wajen matsin lamba wani babban muhimmin abu ne a wajenta. Har ila yau, Iran ta yi ikirarin cewa za a iya samar da zaman lafiya da cigaban tattalin arziki a yankin ta hanyar sabbin dokoki da tsarin gudanarwa na Hormuz, tare da cewa sabon tsarin kula da mashigar zai amfani al’ummar Iran ta fuskar tattalin arziki.
11. Tsohon jakadan Iran a Venezuela, Soltani, ya bayyana cewa kusan ‘yan Iran dubu 700 da ke zaune a Æ™asashen waje sun dawo gida yayin yaÆ™in duk da tsananin hare-haren Amurka da Isra’ila. Ya kwatanta hakan da abin da ya faru a Syria da Iraq, inda ya ce a lokacin yaÆ™e-yaÆ™e mutane kan gudu daga Æ™asarsu, amma a Iran akasin haka ya faru domin mutane sun dawo gida. Soltani ya kuma yi zargin cewa shugaban Mossad ya bai wa Donald Trump tabbacin cewa tarzoma daga cikin gida za ta kifar da gwamnatin Iran, amma ya ce hakan ya zama kuskuren hasashe wanda daga Æ™arshe ya jawo wa Isra’ila matsala a lissafinta. Ya Æ™ara da cewa al’ummar Iran suna haÉ—uwa wuri guda idan wata barazana daga waje ta taso, kuma wannan haÉ—in kai ne ya taimaka wajen kare Iran tsawon dubban shekaru.
12. Tsohon Firayim Ministan Qatar, Hamad bin Jassim Al Thani, ya ce Iran ta fito daga hare-haren Amurka da Isra’ila tana da Æ™arfin siyasa fiye da da. Ya bayyana cewa tunanin kifar da Iran ta hanyar Æ™arfin soja kawai kuskure ne tun farko. Ya kuma ce akwai yiwuwar Iran ta yi amfani da wannan yaÆ™i wajen Æ™ara bunÆ™asa Æ™arfin soja da fasahohinta, sannan ya shawarci Æ™asashen yankin Gulf su ma su Æ™arfafa nasu Æ™arfin domin kare muradunsu.
13. Mai bai wa dakarun IRGC shawara, Birgediya Janar Zolghadr, ya ce maƙiyan Iran sun kasa cimma manufofinsu duk da amfani da hanyoyi da kayan aiki masu yawa. Ya bayyana cewa ƙasashen da ke ikirarin tabbatar da tsaron yankin yanzu suna fama da manyan matsaloli na cikin gida da kuma na ayyukan soja, har ma suna ƙara dogaro da taimakon wasu ƙasashe wajen tura dakarunsu. Zolghadr ya ƙara da cewa abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun fallasa raunin ikirarin manyan ƙasashe masu iko, yana mai cewa zamanin da tura jiragen ruwan yaƙin Amurka kaɗai zai isa ya girgiza ko rusa wata ƙasa ya wuce, domin irin waɗannan matakan ba sa samar da sakamakon dabarun da ake tsammani a yanzu.
— Muhammad Balaa Afuwaa
0 Comments
Drop your thoughts What do you think about this news?