An Hallaka wani ɗan leƙen asirin C/A da M0ssqd a Iran

An Hallaka wani ɗan leƙen asirin C/A da M0ssqd a Iran

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da aiwatar da hukuncin kisa kan Erfan Shakourzadeh bayan samunsa da laifin yi wa Hukumar Leken Asirin Amurka ta C/A da kuma hukumar leƙen asirin Ƙasar Mamaya, M0zzad aiki.

A cewar sanarwar da ma’aikatar shari’ar Iran ta fitar a ranar Litinin, an ɗauki Shakourzadeh aiki a matsayin ma’aikacin wani shiri saboda ƙwarewarsa, a ɗaya daga cikin cibiyoyin kimiyya na ƙasar da ke aiki a fannin tauraron dan adam.

Yayin da yake aiki tare da wannan muhimmiyar cibiyar kimiyya, ya fara hulɗa da hukumomin leƙen asirin maƙiya, ciki har da CIA da musamman Mossad. Bayanai da aka ce ya yi ƙoƙarin miƙa wa maƙiya na cikin sirrikan gwamnati ne, inji Iran.

Rahoton ya ce a farkon matakan hulɗarsa, bayan ya cike fom ɗin haɗin gwiwa da Mossad, Shakourzadeh ya fara musayar bayanai da su ta hanyar imel, inda ya bayar da bayanai na kansa da na iyalansa, wurin aikinsa, irin damar da yake da ita, ayyukan da yake gudanarwa da kuma nauyin da ke kansa a wurin aiki.

Bayan wani lokaci, wani mutum ya sake tuntubarsa ta shafin LinkedIn, yana ikirarin cewa shi ɗan Iran ne da ke zaune a Canada kuma ya ga tarihin aikinsa.
Sai dai daga baya aka gano cewa wannan mutumin jami’in Mossad ne, wanda ya yi masa tayin shiga wasu ayyuka a ƙasashen waje da ake biyan kuɗinsu da dala.
Bayan kulla hulɗa da Mossad, Shakourzadeh ya kuma yi ƙoƙarin tuntuɓar CIA.
Dangane da takardun da aka samu a cikin musayar imel tsakaninsa da jami’in CIA, ya nemi a taimaka masa wajen samun bizar Amurka da kuma damar yin karatu a Amurka.

Ya zuwa yanzu, bamu sami wani cikakken bayani daga ɓangare Amurka da ƙasar mamaya kan kisan ba.

11-05-2026

Post a Comment

0 Comments