Harin dakarun Isra'ila ya kashe mutum uku ƴan gida ɗaya a Gaza, har da Jinjiri 😭

Harin dakarun Isra'ila ya kashe mutum uku ƴan gida ɗaya a Gaza, 

Wani hari da dakarun Isra’ila suka kai a Zirin Gaza ya kashe mutum uku ƴan gida ɗaya, ciki har da wani jinjiri sabon haihuwa.

Rahotanni daga majiyoyin kiwon lafiya sun bayyana cewa Mohammad Abu Mallouh da matarsa Alaa Zaqlan tare da ɗansu jariri Osama sun mutu ne bayan wani hari da aka kai da sanyin safiyar Lahadi a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat.

Majiyoyin sun kuma ce mutane da dama sun samu raunuka sakamakon harin.

Babban asibitin Deir el-Balah da ke tsakiyar Gaza ya tabbatar da karɓar gawarwakin mamatan uku, ciki har da gawar ƙaramin yaro.

Zuwo yanzu gwamnatin Isra’ila ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da harin, duk da zarge-zargen karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma da shiga tsakani na Amurka.

Hukumomin kiwon lafiya a Gaza sun ce hare-haren da ake kaiwa yankin tun daga watan Oktoba sun yi sanadin mutuwar kusan mutum 900.

Post a Comment

0 Comments